Shirin Radio D zango na 2 | Koyon Jamusanci | Deutsche Welle

By: DW.COM | Deutsche Welle
  • Summary

  • Jami'an Radio D sun sake cin karo da wasu Sabbabin matsaloli. A cikin wannan darasi, za mu kasance tare da Paula da Philipp, inda za su zaga cikin Jamus, domin dauko rahoto a kan wani harin hasken wuta da aka kai a garin Jena, da kuma yadda suka bi diddidigin Katangar nan ta Berlin. Wannan bangare na biyu na darasin koyon harshe ya dace da Matakin A2 na Tsarin Koyar da Harsuna na Tarayyar Turai.
    2024 DW.COM, Deutsche Welle
    Show More Show Less
Episodes
  • Kashi na 43 – Shiri na musamman
    Nov 17 2015
    Yanzu an kusan shawo kan matsalar hasken fitilar nan. Sai dai kuma Paula da Philipp ba su ji dadi ba, domin kuwa ga labarin nan duk ya fito a cikin jarida. Ko a ina abokan hamayyarsu suka samo labarin? Paula da Philipp sun ga mummunan labari: akwai cikakken labarin wannan filtila mai mugun haske a cikin wata jarida. Wato, saura su bincike dalilin da ya sa ba a tsaron kofar kamfanin sosai. Sai 'yan jaridar suka nufi wurin. Suna fatan in sun kai za su ga ana hira da 'yan jaridu, ko kuma kakakin kamfanin yana bayani. To, wane ne ya yi hira ke nan? Wannan rudanin ya sa shi ma Farfesa ya yi irin wannan tambaya, sannan kuma ya yi bayani a kan jawabi kai-tsaye da kuma a kaikaice.
    Show More Show Less
    15 mins
  • Kashi na 42 – Aiki ya samu Eulalia
    Nov 17 2015
    Paula da Philipp sun kusa gano wannan al'amari. Yanzu haka dai sun san daga inda mugun hasken nan yake fitowa. Sai dai kuma Eulalia ba ta dawo daga leken asirin da ta tafi ba. Me ya faru? Bayan Paula da Philipp sun gano daga inda hasken yake fitowa, sun sanar da kamfanin fitilun don a warware matsalar. Amma sun fi damuwa da bacewar Eulalia. Sai kawai 'yan jaridun suka ji wani kuka. Ko wani abu ya samu Eulalia ne? Bayan wannan rintsi da aka shiga, yanzu masu saurare za su dan shakata da nazarin kalmomin nahawu. Farfesan yana bayani a kan wakilan suna na mallaka na mutum na uku, wato "sein" da "ihr".
    Show More Show Less
    15 mins
  • Kashi na 41 – Agaji daga sama
    Nov 17 2015
    Wakilan Radio D ba su yi nisa da binciken nasu ba. Sai kawai ga mujiya Eulalia ta bayyana a garin Jena. Watakila za ta iya kawo musu agaji. Paula da Philipp ba za su iya shiga cikin kamfanin fitilun ba saboda ginin na da tsayi. A nan Elulalia take da ranarta tun da za ta iya ganin dakunan binciken kamfanin daga sama. Wannan mujiya mai basira dai ta gano abubuwa da yawa. Amma kuma wani abin ba-zata ya faru. Abubuwan da ke faruwa sun ruda Farfesa ma. Don haka a cikin wannan kashi ya yi bayanin kalmar aikatau mai haska baya, wato "konzentrieren". Wannan wata dama ce ta nazarin wakilan suna masu haska baya.
    Show More Show Less
    15 mins

What listeners say about Shirin Radio D zango na 2 | Koyon Jamusanci | Deutsche Welle

Average customer ratings

Reviews - Please select the tabs below to change the source of reviews.